NE

News Elementor

Sanata mai wakiltar Borno ta kudu, Mohammed Ndume, ya buƙaci rundunar sojin Najeriya da ta ƙara ƙaimi wajen ceto mutanen da akayi garkuwa da su a jihar Borno

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Mohammed Ndume, ya buƙaci rundunar sojin Najeriya da ta ƙara ƙaimi wajen ceto ɗaliban makaranta da matafiya da aka yi garkuwa da su a wasu al’ummomin kudancin jihar.


Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Ndume ya ce wasu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su sun shafe sama da kwanaki 100 a hannun masu garkuwa da mutanen.


Sanatan ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyara hedikwatar rundunar Operation Hadin Kai ta Arewa maso Gabas da ke Maiduguri ranar Laraba, inda ya yaba wa sojojin bisa ƙoƙarin da suke yi wajen yaƙi da ’yan ta’adda.


Ndume ya ce roƙon nasa ya shafi ɗaliban da aka sace daga Mussa da Lassa a Ƙaramar Hukumar Askira Uba, fasinjojin da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Buratai, da kuma sauran waɗanda har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutane daga Ngoshe a Ƙaramar Hukumar Gwoza.


Ya ce duk da cewa ya san sojoji na yin iya ƙoƙarinsu, tsawon lokacin da waɗannan mutane suka yi ba tare da komawa ga iyalansu ba ya ƙara haifar da fargaba da damuwa ga ’yan uwansu da al’ummominsu.


Sanatan ya ce wasu daga cikin waɗanda aka sace sun shafe fiye da kwanaki 100 ba tare da ganin iyalansu ba, lamarin da ya ce ya haifar da matuƙar damuwa a tsakanin ’yan uwa da al’ummomin da abin ya shafa.


Sai dai Ndume ya bayyana cewa kiran da yake yi bai kamata a ɗauke shi a matsayin rashin amincewa da sadaukarwar da sojoji ke yi ba, sai dai nauyin da ya rataya a wuyansa na ci gaba da magana a madadin mutanensa da kuma neman ɗaukar mataki a kan matsalolin da suke fuskanta.


Ya ce zai ci gaba da yabawa sojojin idan suka yi abin da ya dace, tare da gabatar musu da damuwar mutanen mazabarsa domin a ƙara ƙoƙarin ganin an ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM