Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da harin da aka kai a kauyen Naridon da ke gundumar Kamaru, a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
Shugaban ya kuma umarci hukumomin tsaro da na tattara bayanan sirri da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu a yankunan da lamarin ya shafa domin gano wadanda suka aikata laifin tare da kubutar da duk mutanen da aka yi garkuwa da su.
Harin, wanda ya faru da sanyin safiyar ranar Litinin, ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 30 da suka hada da mata da kananan yara, yayin da aka kuma banka wa gidaje da dama wuta.
A cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan harkokin yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, ya bayyana harin a matsayin ta’addanci da aka kai ba tare da wata tsokana ba kan fararen hula da ba su ji ba su gani ba.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa duk wadanda ke kokarin kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron da jihar Kaduna ta fara samu a baya-bayan nan za a kamo su tare da gurfanar da su a gaban shari’a.
Ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasu, Gwamna Uba Sani, gwamnatin jihar Kaduna da daukacin al’ummar jihar bisa wannan mummunan al’amari.
Shugaban ya tabbatar wa gwamnatin jihar da al’ummomin da abin ya shafa cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ba su goyon baya wajen shawo kan matsalolin tsaro a fadin kasar nan.