Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ce Amurka tana cikin shirin ko-ta-kwana domin ɗaukar mataki idan har Iran ta kashe masu zanga-zangar lumana, bayan zanga-zangar tsadar rayuwa a ƙasar ta rikide zuwa tashin hankali.
Masu zanga-zanga da jami’an tsaro sun yi arangama a wasu biranen Iran a ranar Alhamis, inda rahotanni suka ce mutane shida sun rasa rayukansu kuma su ne na farko tun bayan da rikicin ya ƙara tsananta.
A babban birnin ƙasar, Tehran, ‘yan kasuwa sun shiga yajin aiki a ranar Lahadi domin nuna fushinsu kan tsadar kayayyaki da tabarbarewar tattalin arziki.
Wannan mataki ya bazu zuwa wasu sassan ƙasar.
Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa, “Idan Iran ta yi harbi tare da kashe masu zanga-zangar lumana cikin tashin hankali, wanda hakan dabi’arsu ce, to Amurka za ta kai musu ɗauki.”
