Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga iyaye, shugabanni da al’umma gaba ɗaya da su haɗa kai wajen kawo ƙarshen auren wuri tare da tabbatar da kare haƙƙoƙin ƴaƴa mata.
Ta bayyana haka ne a saƙon ranar bikin Ranar ‘Yar Mace ta 2026, wanda aka gudanar a ƙarƙashin taken “kawo ƙarshen auren yara da zuba jari a kula da haƙƙoƙin ƴaƴa mata,” inda ta ƙara da cewa buƙatar bai wa kowace yarinya damar samun ilimi, kiwon lafiya da kuma yanayin da zai ba ta damar cimma burikanta.
Ta jaddada cewa kowace ƴar mace na da haƙƙin yin karatu, girma da kuma gina makomarta ba tare da fuskantar wariya, tashin hankali ko wasu munanan al’adu da ke hana ta cimma burinta ba.
Sanata Oluremi Tinubu ta yi kira ga iyalai, al’umma, shugabannin addini da na gargajiya, da masu tsara manufofi da su ɗauki matakan kare haƙƙin ‘ya’ya mata tare da kawo ƙarshen auren yara, wanda ke hana yara mata damar cigaba da karatu da samun ingantacciyar rayuwa.
Ta ce idan aka bai wa ‘ya’ya mata damar bunƙasa da cimma burinsu, hakan zai amfani iyalai, al’umma da kuma ƙasa baki ɗaya.
“Lokacin da ‘ya’ya mata suka samu damar bunƙasa, iyalai suna samun ci gaba, al’umma suna ƙara ƙarfi, ƙasa kuma tana samun cigaba mai ɗorewa,” in ji ta.