NE

News Elementor

’Yan kasuwar mai sun ce matatar Dangote kaɗai ba za ta wadatar da Najeriya da man fetur ba

Manyan dillalan man fetur a Nigeri sun nace cewa duk da rage farashin man fetur da matatatr man fetur ta Dangote ta yi a kwanan nan da kuma kara yawan man da take fitarwa a cikin gida, hakan ba zai wadatar da kasar nan  da man fetur ba, inda suka yi gargadin cewa dogaro da hanya guda ta samar da man fetur tuni da ya fara haifar da matsaloli a kasuwar mai.

Sakataren Zartarwa na kungiyar yan kasuwar mai a Nigeria, Mista Clement Isong ne ya bayyana hakan, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan tasirin rage farashin mai da Matatar Dangote ta yi, inda ta rage farashin daga naira ₦828 zuwa naira ₦699 kan kowace lita, abin da ya sa farashin ya sauka a gidajen mai zuwa kusan ₦739 kan kowace lita a gidajen mai da ke hulda da matatar Dangote.

Isong ya ce duk mambobin kungiyar ta MEMAN a halin yanzu suna sayen man fetur daga Matatar Dangote, amma ya jaddada cewa ƙalubalen samun man da matsalolin sufuri da bata lokaci sun sa ba zai yiwu matatar ta zama ita kadai c eke samar da mai a kasar nan ba.
Ya kuma ce hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa ta yi shiri mai kyau a lokacin bukukuwan Kirsimeti ta hanyar bayar da lasisin shigo da mai daga waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM