Hukumomi a arewacin Mali sun ce mayaƙan Tuareg masu neman ɓallewa da kuma mayaƙan ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi sun kashe aƙalla sojojin Mali 50 a wani kwanton-ɓauna da suka yi wa ayarin motocin soji a ranar Asabar da ta gabata.
Sun kuma ce maharan sun yi garkuwa da sama da mutum 20 a yayin harin.
Wannan bayani na jami’an yankin ya yi daidai da ikirarin da Azawad Liberation Front (FLA) ta yi cewa mayaƙanta sun yi wa sojojin Mali da kuma dakarun Rasha da ke mara musu baya mummunar illa.