Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a kafar yaɗa labarai ta DCL Hausa a daren ranar Laraba.
Ya ce ba ya adawa da cire tallafin man fetur, sai dai yana tambayar inda kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin suka shiga.
A cewarsa, ya kamata a yi amfani da kuɗaɗen wajen rage talauci, taimaka wa yara da ba sa zuwa makaranta da kuma inganta rayuwar ’yan Najeriya.
Atiku ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da kasancewa cikin gwamnatocin da ake zargin an samu yawan cin hanci da rashawa, yana mai cewa ana karkatar da kuɗaɗen gwamnati.
Ya ce idan aka ba shi damar jagorantar Najeriya, duk wanda ya saci kuɗin gwamnati zai tilasta masa ya dawo da su, domin tabbatar da cewa dukiyar ƙasa tana amfani wajen inganta rayuwar jama’a.
Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023, jim kaɗan bayan rantsar da shi, matakin da ya haifar da tashin farashin man fetur da kuma ƙara tsadar rayuwa a Najeriya.
Gwamnatin Tinubu ta sha kare matakin cire tallafin, tana mai cewa ya taimaka wajen rage nauyin da gwamnati ke fuskanta wajen biyan tallafin. Sai dai Atiku ya buƙaci a bayyana yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin, yana mai cewa bai kamata ’yan Najeriya su faɗa cikin matsanancin hali ba. Aminiya ce ta rawaito.