Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA) ta bayyana cewa wasu daliban likitanci yanzu suna fara shirin barin Najeriya zuwa kasar waje tun kafin su kammala karatunsu, sakamakon rashin kyakkyawan yanayin aiki da makoma a fannin lafiya.
Shugaban NMA, Farfesa Afekhide-Ernest Omoti, ya ce wasu daliban na fara rubuta jarabawar cancantar aiki a kasashen waje tun lokacin koyon aikin likitanci, domin su samu damar yin hijira bayan sun kammala rajista.
Omoti ya ce ana bukatar Gwamnatin Tarayya ta inganta albashi, tsaro, kayan aiki da jin dadin likitoci domin dakile yawan barin kasar da kwararrun ma’aikatan lafiya ke yi.
Ya ce NMA ta gabatar wa gwamnati da shawarar samar da wani tsarin kulawa da walwalar likitoci da zai sa su ga dalilin ci gaba da aiki a Najeriya.
Shugaban NMA ya kuma yi gargadin cewa gwamnati na kashe makudan kudade wajen horar da likitoci, amma daga bisani su bar kasar zuwa kasashen waje, lamarin da ya ce yana jefa tsarin kiwon lafiyar Najeriya cikin hadari.
Haka kuma, ya yi kira da a kara tsaro a asibitoci domin kare likitoci daga hare-hare da cin zarafi, musamman a sassan kula da marasa lafiya na gaggawa.