NE

News Elementor

Ƴan Bindiga Sun Kashe Sama Da Mutum 50 Bayaga Wasu Da Suka Sace A Jihar Zamfara

Ɗan majalisar da ke wakiltar Bukkuyum ta kudu a majalisar dokokin jihar Hamisu A. Faru ne ya tabbatarwa Kamfanin Dillancin Labarai na Rueters faruwar lamarin, inda ya ce tun da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Alhamis maharan suka shiga garin Tungan Dutse har zuwa ƙarfe 3 da rabi na safiyar jiya Juma’ar nan.

Ya ce ƴan binda sun kona gidaje da dama sannan suka rinƙa harbin waɗanda suka yi ƙoƙarin gudu daga garin.

Ɗan majalisar ya ce kawo yanzu basu kammala aikin tantance adadin waɗanda aka sace ba, amma dai masu riƙe da sarautun gargajiya da kuma jami’an ƙaramar hukumar na ci gaba da aiki akan hakan.

Wani mazaunin garin na Tungan Dutse Abdullahi Sani, ya sheda wa Rueters cewa daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu, akwai ƴan uwansa uku.

Ya ce ana gobe abin zai faru sun shaida wa hukumomin tsaro da kuma jami’an ƙaramar hukumar cewar, sunga wasu mutane kan babura sama da 150 ɗauke da makamai, amma kuma ba a ɗauki wani mataki akai ba.

Jihar Zamfara dai, na daga cikin jihohin da ke fama da matsalolin tsaro a Arewacin Najeriya, inda ake samu asarar rayuka masu yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM