NE

News Elementor

Ƴansanda sun sun ƙwato bindigogi a wajen wani da a ke zargin ɗan fashi da makami ne a jihar Rivers

Rundunar ƴansandan Jihar Rivers ta kama wani da ake zargin ɗan fashi da makami ne tare da ƙwato bindigogi da alburusai a wani samame da ta gudanar bisa sahihan bayanan sirri.

Kakakin rundunar, ASP Agabe Blessing-Kaborlo, ya ce an kama wanda ake zargin, Austine Emenike, wanda aka fi sani da “Oyibo”, ɗan ƙauyen Aluu a jihar Rivers.

Kayayyakin da aka ƙwato daga hannunsa sun haɗa da bindiga ƙirar gida guda ɗaya, bindigogi masu harsashi guda huɗu da alburusai guda biyar.

Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana da alaƙa da wata babbar ƙungiyar masu aikata laifuka, kuma jami’an bincike na ci gaba da neman sauran mambobin ƙungiyar.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Olugbenga Adepoju, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da samamen, tare da jaddada cewa rundunar ba za ta bai wa masu aikata laifuka mafaka a jihar ba.

Ya kuma buƙaci mazauna jihar su riƙa kai rahoton duk wani mutum ko motsi da suke zargin yana da alaƙa da aikata laifi domin taimaka wa jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM