NE

News Elementor

Ɗan Majalissa Ya Raba Motocin Miliyan 360 Ga Malamai 12 A Zamfara

Wani ɗan Majalisar tarayya, Abdulmalik Zubairu na jam’iyyar APC a jihar Zamfara, ya bai wa malamailn addinin Musulunci 12 a sabbin motoci kirar Toyota Camry, waɗanda darajarsu ta kai Naira miliyan 360.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya,NAN ya ruwaito cewa Zubairu, shi ne ɗan majissar wakilai mai wakiltar mazabar Bungudu da Maru a majalisar tarayya.

Daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin motocin akwai Abdullahi Dalla-Dalla da Na’Allah Zurmi da Usman Tambuwal da Atiku Zawiyya da Yusuf Dinawa da Abubakar Sodangi da da Ibrahim Zawiyya.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, wanda ya miƙa motocin ga waɗanda suka amfana a madadin ɗan majalisar, ya yaba da wannan kyakkyawan karamci da Abdulmalik Zubairu ya nuna na tallafa wa malaman addinin Musulunci a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan kallon masu sukar ta a matsayin makiya

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta daina kallon duk masu sukar manufofinta a matsayin makiyan Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta rika karɓar suka mai ma’ana. Sanusi ya bayyana haka ne yayin wani taron shugabanci na Oxford Global Think Tank Leadership Conference da aka...

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM