NE

News Elementor

“ƙarairayi da ne ta yi ba zaman lafiya a Sokoto, na yi tuƙi tun daga garin Sokoto har garin Silame ba mu ga wani bandit ko ƙwara ɗaya ba tak a hanya” – Abdullahi Sule, Gwamnan Jihar Nasarawa

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya musanta rahotannin da ke cewa jihar Sokoto ba ta cikin yanayin zaman lafiya, yana mai cewa ya tuka mota daga garin Sokoto zuwa Silame ba tare da ganin ɗan bindiga ko ɗaya ba.

Sule ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da wani aiki a ƙaramar hukumar Silame ta jihar Sokoto.

Ya ce labaran da ake yadawa game da rashin tsaro a Sokoto na iya tsoratar da masu zuba jari, musamman waɗanda ke son zuwa jihar daga wasu ƙasashe.

A cewarsa, wasu daga cikin rahotannin da ake bayarwa ba su nuna cikakken yanayin tsaro na jihar ba, lamarin da ya ce kan sa masu zuba jari su fasa zuwa.

Gwamnan ya ce babu wata jiha da za a ce ba ta fuskantar wata matsalar tsaro ko ta zamantakewa, yana mai cewa har da jihar Legas, inda ya taɓa aiki a baya, tana fuskantar nata ƙalubalen.

Ya kuma zargi ‘yan siyasa da amfani da kalamai marasa tushe wajen ƙara dagula al’amura da kuma tsoratar da masu son zuba jari.

Sule ya ce irin waɗannan maganganu na iya yin illa ga tattalin arzikin jihohi, domin masu zuba jari daga cikin gida da ƙasashen waje na iya janye shirinsu saboda tsoron rashin tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM