Yan bindiga sun kai hari a kauyen Dangoro dake mazabar Nahuce a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara, inda suka kashe mutum 3, da sace wasu da dama, kazalika da kona gidaje da rumbunan abinci.
Mazauna kauyen sun ce maharan sun farmake su ne a daren ranar Lahadi, inda suka rinka harbi mai kan uwa da wabi.
Daga cikin wadanda aka kashe har da wata mata mai juna biyu dan wata 9, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Har kawo yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba, amma kuma mafiyawa mata ne.
Bayanai sun ce maharan sun kuma gona gidaje da rumbunan abinci, lamarin da ya tilastawa mazauna kauyen guduawa zuwa garin Nahuce domin neman mafaka.
Wani mazauni kauyen da ya bukaci a Sakaye sunansa, ya ce yanzu haka alumma na cikin fargaba bayan yan bindigar sun yi barazanar sake komawa.