NE

News Elementor

Amurka Ta Kai Hare-hare Kan Cibiyoyin Kungiyar ISIS A Syria

Sojojin Amurka sun kai hare-hare kan sama da wurare 70 na ƙungiyar Islamic State (ISIS) a kasar Syria ranar Juma’a, a abin da Shugaba Donald Trump ya bayyana a matsayin “ramuwar gayya mai tsanani” biyo bayan wani hari da ya kashe ‘yan Amurka uku a ƙarshen makon da ya gabata.

Washington ta ce wani ɗan bindiga guda daga ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya ne ya kai harin ranar 13 ga Disamba a Palmyra, wurin da ke ɗauke da tsoffin gine-ginen tarihi da UNESCO ta amince da su, kuma a da yana ƙarƙashin ikon masu ikirarin jihadi wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Amurka biyu da kuma wani ɗan ƙasar Amurka farar hula.

A martani, Amurka ta ce “ta kai hare-hare kan fiye da wurare 70 a wurare daban-daban a tsakiyar Syria ta hanyar amfani da jiragen yaƙi, jiragen sama masu saukar ungulu na yaƙi, da kuma manyan makamai,” kamar yadda Rundunar CENTCOM ta bayyana a cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “an yi amfani da harsasai sama da 100 wajen kai hare-haren, waɗanda aka nufe kai wa kan wasu cibiyoyin ISIS da wuraren ajiye makamai,” in ji CENTCOM.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM