Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana jin daɗinsa kan sabon jerin matsayi na tattara kuɗaɗen shiga da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa NBS ta fitar, wanda ya sanya Jihar Kano a matsayi na tara a faɗin ƙasa, kuma ta ɗaya a Arewacin Najeriya.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Asabar.
Gwamna Yusuf ya bayyana farin cikinsa ne a lokacin da Shugaban Hukumar Tattara Harajin Cikin Gida ta Jihar Kano (KIRS), Zaid Abubakar, ya yi masa bayani kan wannan matsayi yayin bikin rantsar da sabbin ma’aikatan KIRS da aka ɗauka aiki, wanda aka gudanar a dakin taro na Coronation Hall, da ke Fadar Gwamnatin jihar Kano.
A cewar Abubakar, wannan matsayi ya samo asali ne daga sabon rahoton ƙididdiga da NBS ta fitar, wanda ke nuna gagarumin ci gaban da aka samu a harkar tattara kuɗaɗen shiga na jihar.
“Yau Jihar Kano ta zama ta ɗaya a Arewacin Najeriya, kuma ta tara a faɗin ƙasa wajen tattara kuɗaɗen shiga. A baya mun taɓa kasancewa har matsayi na 30,” in ji shi.
Shugaban KIRS ya bayyana wannan nasara a matsayin sakamakon sauye-sauyen da gyare-gyare da ake aiwatarwa a ɓangaren tattara kuɗaɗen shiga a ƙarƙashin wannan gwamnati.
Ya yaba wa Gwamna Yusuf bisa jajircewarsa wajen gyaran hukumomi, ƙwarewa da ɗa’a a aikin gwamnati, da kuma ɗaukar harkar tattara kuɗaɗen shiga a matsayin muhimmin ginshiƙi na ci gab mai ɗorewa.
Sanarwar ta bayyana cewa ɗaukar ma’aikata 120 na dindindin masu samun fansho a muhimman sassan hukumar tattara kuɗaɗen shiga—ciki har da ƙwararru a fannonin tattalin arziƙi, lissafi da haraji—wani mataki ne na musamman domin dorewa da ƙara inganta matsayin kuɗaɗen shiga na jihar.
Ya jaddada cewa jarin da gwamnan ya zuba a ɓangaren bunƙasa ƙwarewar ma’aikata zai ƙarfafa tsarin gudanar da kuɗaɗen shiga da ingancin ayyuka.
Gwamna Yusuf ya yi gargaɗin cewa gwamnatinsa ba ta da sassauci ko kaɗan kan cin hanci da rashawa, amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba, ko ɗabi’u marasa kyau, yana mai cewa duk wani jami’i da aka samu da laifi zai fuskanci matakan ladabtarwa da suka dace.
A nasa jawabin, Kwamishinan Kuɗi, Dr Ismail Aliyu Danmaya, ya taya sabbin ma’aikatan da aka rantsar murna tare da jaddada cewa ingantacciyar tafiyar da harkar tattara kuɗaɗen shiga na da matuƙar muhimmanci ga ajandar ci gaban Jihar Kano.
