NE

News Elementor

Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Biya Iyalan Wadanda Harin Jirgin Sama Ya Shafa

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta biya diya ga mutanen da iyalansu suka shiga matsala sakamakon harin sama da aka kai bisa kuskure a ranar 25 ga Disamba, 2024, a jihar Sokoto.

Wadanda abin ya shafa sun haɗa da mazauna ƙauyukan Gidan Bisa da Rumtuwa da ke ƙaramar hukumar Silame a jihar.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.

A yayin jawabinsa, Babban Hafsan Sojin Sama (CAS), Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, wanda Babban Jami’in Hulɗar Soja da Fararen Hula, AVM Edward Gabkwet, ya wakilta, ya nuna godiya ga gwamnatin jihar bisa kyakkyawar alaƙa da ke tsakanin NAF da al’ummar jihar.

Ya yaba wa Gwamna Ahmed Aliyu kan manufofin ci gaba da suka haɗa kowa da kowa da kuma matakan tsaro da gwamnatin jihar ta ɗauka a ƙarƙashin ajandar 9-Point Smart Agenda, musamman kafa rundunar Sokoto State Community Guards Corps.

Babban Hafsan ya ce matakan tsaron da gwamnan ya ɗauka na kusa da al’umma sun taimaka wajen ƙarfafa ƙoƙarin gwamnatin tarayya na daƙile ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga, lamarin da ya inganta tsaro a wasu sassan jihar tare da nuna muhimmancin kyakkyawar hulɗa tsakanin sojoji da fararen hula.

Ya bayyana cewa harin saman da aka kai ya kasance ne a ƙarƙashin Operation Fasan Yamma, bayan samun bayanan leƙen asiri da ke nuna cewa ana zargin ’yan ta’adda masu makamai na wucewa ta cikin al’ummomin da abin ya shafa.

A cewarsa, duk da cewa an gudanar da binciken leƙen asiri sau da dama kafin kai harin, wani ƙorafi da aka karɓa a watan Afrilun 2025 ya nuna cewa an samu asarar rayukan fararen hula.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM