NE

News Elementor

Shugaban Kasa Ya Sauka A Lagos Domin Hutun Sabuwar Shekara

Shugaban kasa Bola Tinubu ya isa birnin Legas domin hutun karshen shekara.

Tsohon gwamnan jihar Legas din ya isa filin jirgin saman Murtala Muhammad da daren jiya Assabar, bayan ziyarar da ya kai a jihohin Borno da Bauchi.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas ne ya tarbe sa tare da rakiyar sauran jami’an gwamnatin jihar.

Kazalika an tanadi masu kade-kade da su ka yiwa shugaban rakiya har zuwa cikin birnin Ikko, inda zaiyi hutunsa na sabuwar shekara.

Mai Magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya ce magidansa zai halarci taruka daban-daban ciki har da bukin al’ada na Eyo.

Zai kuma karbi manyan mutane daga sassan kasar nan wadanda za su rinka kai masa ziyarar murnar sabuwar shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM