Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kashe ’yan bindiga sama da 23 ta hanyar kai musu farmakin jiragen yaƙi, a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa daga Jihar Kano zuwa Jihar Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne bayan ingantattun bayanan sirri da suka tabbatar da motsin ’yan bindigar, inda jiragen sojin suka yi nasarar kai farmaki a kan tawagar yayin da suke tsaka da tserewa.
Majiyoyi na tsaro sun bayyana cewa farmakin ya yi babbar nasara, lamarin da ya taimaka wajen raunana ƙarfinsu da hana su sake shirya hare-hare a yankunan da ke makwabtaka da Kano da Katsina.
Hukumomin tsaro sun jaddada cewa za su ci gaba da kai farmaki ba tare da sassauci ba kan duk wata ƙungiyar ’yan bindiga, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da dawo da zaman lafiya a yankunan Arewa maso Yamma.