NE

News Elementor

Tinubu Ya Taya Gwamna Yusuf Murna Cika Shekaru 63 Da Haihuwa

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aikawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, saƙon taya murnar zagayowar ranar haihuwarsa a ranar Lahadi, inda ya yaba da “amincinsa, tawali’u, ƙanƙantar kai da kuma jajircewarsa wajen hidimta wa jama’a.

Tinubu ya isar da saƙon ne ta cikin wata sanarwa da hadiminsa kan sha’anin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu.

Saƙon taya murnar ranar haihuwar Gwamna ya zo ne sa’o’i kaɗan bayan sanarwar dage shirin ficewar Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, wanda tun farko aka tsara zai gudana a ranar Litinin, 5 ga Janairu, 2026—ranar cikarsa shekaru 63—amma aka mayar da shi zuwa ranar 12 ga Janairu.

A cikin sanarwar, Tinubu ya yabawa gwamnan Kano kan nasarorin da ya samu wajen bunƙasa ababen more rayuwa da kuma jajircewarsa wajen ci gaban al’umma.

Sanarwar ta ce Ƙwarewar shugabanci da Gwamna Yusuf ya samu, musamman shekaru da ya shafe yana kwamishina yana kula da muhimman ma’aikatu a Jihar Kano, na yi masa jagoranci ga iri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM