
Gwamnatin tarayya ta kashe akalla naira triliyan 7 a bangaren wutar lantarki daga shekarar 2013 zuwa yanzu, lokacin da ta cefanantar da fannin domin inganta harkokin lantarki a Nigeria.
To sai dai, duk wannan makudan kudin da aka kashe, har yanzu Nigeria ta kasa samun tsayayyar wutar lantarki.
Ko a watan farko na wannan sabuwar shekara, sau biyu alummar kasar nan na fadawa cikin duhu sakamakon lalacewar babban layin wuta na kasa.
A gwamnatocin da suka gabata, adadin wutar da ake samarwa ta yi kasa zuwa megawatt 1,800, yayin da suma turaku da layukan da ake amfani da su wajan rarraba wutar ke fuskantar babban kalubale.
Dukkan gwmanatocin da suka gabata tun daga 1999 zuwa yanzu, sun bada fifiko wajan inganta wutar lantarki a Nigeria, inda har ministan makamashi na farko a zamanin Olusegun Obasanjo, Chief Bola Ige ya yi alkawarin magance matsalar a cikin kankanen lokaci.
To sai dai, gwamnatin Obasanjo ba iya kasa cika wannan burin nata ta yi ba, har ma abubuwan sun kara durkushewa a karkashin ikonta.