Shirin tallafawa yaya mat ana AGILE ya kammala ayyuka 94 daga cikin 161 da ya tsara yi a shekarar 2025 a jihar Sokoto.
Shugaban shirin na jiha, Dr Mansur Buhari ne ya bayyana hakan a yayin tattaunawa da manema labarai.
Da yake samun wakilcin mataimakin manajan shirin mai kula da tsare-tsare, Malam Suleiman Musa, Mansur ya ce sun kashe naira biliyan 8.4 a shekarar 2025.
Dr Mansur ya ce shirin AGILE ya gyara azuzuwa 749, da gina riyojin murtsatse masu amfani da hasken rana kimanin 214 a fadin makarantun 240, kazalika da gina ban-dakuna 1,652 a fadin kananan hukumomi 23 na jihar Sokoto.
Shugaban shirin ya ce sun dasa bashiyoyi kimanin 4,480 a makarantu 224, tare da saka yan mata 16,528 a makarantu daga cikin yara 17,000 da aka yi hasashen samu, da samar da kujeru 11,221 a makarantu, kazalika da samar da kayan karatu kimanin 97,446 a fadin makarantu 240.