Jam’iyyar APC ta naɗa tsohon Gwamnan Jihar Katsina kuma tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Aminu Masari, a matsayin Shugaban Kwamitin shirya Babban Taron Ƙasa na jam’iyyar da ake sa ran gudanarwa a watan Maris.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa daga ofishin wakataren yaɗa labarai na Ƙasa na jam’iyyar, wadda aka fitar a ranar Juma’a a Abuja.
Jam’iyyar ta kuma faɗaɗa jerin shugabancin Kwamitin l Tsara Ayyuka (Central Coordination Committee) na taron daga mambobi 73 zuwa 90.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Anyim Pius Anyim, zai kasance Mataimakin Shugaba na Ɗaya, tare da Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), yayin da Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, zai kasance Mataimakin Shugaba na Biyu.
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, zai kasance Sakataren Kwamitin.
Sanata Hope Uzodimma, Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC wanda tun da farko aka sanar da shi a matsayin Shugaban Kwamitin, yanzu zai riƙe muƙamin Ma’aji.
Kwamitin da aka sake tsarawa ya haɗa da dukkan gwamnonin APC guda 27 masu ci, tsohon Shugaban jam’iyyar, Cif Bisi Akande, Sanata Adams Oshiomole, Sanata Abdullahi Adamu, da Dokta Abdullahi Ganduje.