NE

News Elementor

karuwar Rashin Tsaro A Nigeria Na Nuna Cewa Babu Gwamnati A kasar Nan – Bolaji Abdullahi

Mai Magana da yawun jamiyyar ADC, kuma tsohon ministan matasa da wasanni, Mallam Bolaji Abdullahi ya ce karuwar rashin tsaro a Nigeria na nuna cewa babu gwamnati a kasar nan.

Abdullahi na tsokaci ne kan wani sako da shugaban kasa Bola Tinubu ya wallafa a shafin X a shekarar 2014, inda ya koka kan kazantar rashin tsaro karkashin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.Tinubu, wanda a lokacin babban dan adawa, ya sha sukar manufofin gwamnatin Jonathan, musamman bayan bullar hare-haren Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

Da yake tsokaci kan tsohon sakon, Abdullahi ya ce sabbin hare-haren da ake fuskanta a halin yanzu na nuna cewa babu gwamnati a Nigeria.

Ya kara da cewa, kashen da ke faruwa a Kwara, Katsina da sauran sassan kasar nan, kazalika da kisan kiyashin da ake yiwa yan Nigeria a kusan kullum, babban dalili ne dake tabbatar da cewa babu gwamnati a Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM