yarjejeniya ta dabarun tsaron kan iyaka, kare kayayyakin da ke wucewa ta iyakoki da kuma bunƙasa hulɗar tattalin arziƙi.
Babban Kwanturola Janar na hukumar kwastam na Nijeriya Bashir Adeniyi, ne ya bayyana hakan a wani babban taron tattaunawar haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Kwastam ta Nijeriya da Hukumar Kwastam ta Jamhuriyar Nijar da aka gudanar a Abuja. Tawagar Nijar ta samu jagorancin Darakta Janar ɗinta, Muhammadu Yaqouba.
Adeniyi ya ce haɗin gwiwar za ta mayar da hankali ne kan sauƙaƙa kasuwancin yankin, kare kayayyakin da ke wucewa, ƙarfafa musayar bayanai, da inganta haɗin gwiwar tsaro a kan iyaka.
A cewarsa, an tsara wannan haɗin gwiwa ne domin inganta jigilar kayayyakin da ake kaiwa Jamhuriyar Nijar ta hanyar Nijeriya, magance matsalolin tsaro a kan iyakokin ƙasashen biyu, da rage jinkiri a manyan hanyoyin wucewar kayayyaki, domin tabbatar da cewa halastaccen kasuwanci yana ba da gudunmawa yadda ya kamata ga bunƙasar tattalin arziƙin ƙasashen biyu.