NE

News Elementor

Rikicin Gabas Ta Tsakiya Ya Jefa Matafiya Aikin Umrah Cikin Rudani

Rashin tabbas ya mamaye masu yunkurin zuwa Umarah a Nigeria, a yayin da rikicin Iran da Amurika ke ci-gaba da kassara zirga-zirgar jiragen sama.

Rahotanni sun ce dimbin musulmi ne ke yin umarah a cikin Ramadan, inda a bara aka samu akalla mutum miliyan 122 da su ka yi ibadar.

To sai dai, rikicin da ake fuskanta a gabas ta tsakiya, baya ga rufe sararin samaniyar manyan kasashe irin Doha da Dubai, na tilastawa yan Nigeria sauya tsarin tafiyar tasu.

Tuni lamarin ya haddasa damuwa game da yanayin kariya da lokutan da za a shafe kafin tashi da saukar jirgi, inda mutane da dama ke shakku game da zuwa umarah a wannan shekara.

Daga cikin manyan kamfunnan jiragen sama da suka dakatar da zirga-zirga akwai Emirates, Etihad, Qatar Airways, Air France, British Airways, Syria Air, Air India, Turkish Airlines, EgyptAir, Lufthansa da kuma Ethiopia Airlines.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM