Shugaban kasar Iran Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafin X, bayan abin da ya kira hare-haren Amurika da Isra’ila kan makarantu da asibitoci a Tehran.
A cewarsa, an kashe daliai 168 a watan asibitin kasar, amma kuma hukumomin Amurika ko Israila ba su tabbatar da hakan ba.
A halin da ake ciki kuma, gwamnatin Amurika ta ce Iran za ta fuskanci karin hare-hare a yan kwanaki kadan masu zuwa.
Sakataren harkokin wajen kasar, Marco Rubio ya shedawa manema labarai cewa, dakarun Amurika za su harba karin makamai, kuma abubuwan da za su biyo baya za su yi muni sosai.
Babban jami’in na diplomasiyya ya ce Amurika ta dauki matakin ne domin kare duniya daga barazana.