Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta ce a dangantakarta da duk wanda bai san Allah ba ko kuma bai ji tsoronsa ba ba ta daɗewa.Matar Shugaban Ƙasar ta kuma bayyana cewa cikin kusan shekaru 40 da ta yi tana aure da Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, wanda Musulmi ne, ba ta iya tuna wani lokaci da ɗayansu ya taɓa ɗaga wa ɗaya murya ba.Sanata Oluremi Tinubu ta faɗi hakan ne lokacin da ta karɓi baƙuncin taron buda baki na addinai daban-daban a Old Banquet Hall da ke Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.Taron buda bakin ya samu halartar mabiya manyan addinan ƙasar biyu — Kiristoci da Musulmi — tare da matan gwamnonin.