NE

News Elementor

NDLEA Ta Kama Wani Tsohon Kansila A Legas Da Tabar Wiwi Kilo 40

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya, NDLEA, ta kama Sheleru Sadiq, tsohon kansila a yankin Orimedu da ke ƙaramar hukumar Ibeju-Lekki a jihar Lagos , bisa zargin mallakar wiwi kilo 40.

Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya ce an kama Sadiq a gidansa a ranar 2 ga Maris, inda jami’an suka gano wiwi nau’in skunk kilo 40 a ɗaya daga cikin ɗakunan gidan. Ya kuma amsa cewa kayan da gidan nasa ne.

A cewar NDLEA, Sadiq wanda a yanzu yake aiki a matsayin mataimakin majalisa, ya taɓa yin wa’adin kansila sau biyu yana wakiltar al’ummar Orimedu.

A wani samame dabam, jami’an NDLEA sun kuma kama Emeka Hyginus Okwor da ƙwayoyi 1,000 na tapentadol da aka ɓoye a cikin pampers na jarirai, yayin da aka kama wani ɗan Kamaru, Mey Ali Muhamat, da miyagun ƙwayoyi a jihar Kogi .

Haka kuma jami’an sun kama Osama Abdullahi a jihar Niger bayan gano sassan na’urar fashewa (IED) guda 500 a cikin wata motar haya.

Bugu da ƙari, jami’an sun ƙwato ƙwayoyin tramadol 122,000 da gram 700 na methamphetamine a jihar Adamawa , yayin da aka kama wasu da miyagun ƙwayoyi a jihohin Kano da Ogun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM