NE

News Elementor

Dangote Ya Ce Rikicin Gabas Ta Tsakiya Zai Iya Sa Yan Najeriya Su Koma Rayuwa Irin Ta Lokacin Covid-19

Shugaban kamfanin Dangoye, Aliko Dangote ya yi gargadin cewa, rikicin gabas ta tsakiya zai iya tilastawa Nigeria da sauran kasashen Africa komawa aiki daga gida kamar yadda aka yi a zamanin Covid-19.

Dangote ya bayyana hakan ne bayan ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a gidansa dake Legas, inda ya bayyana damuwa game da tasirin tattalin arziki da kuma yanayin tashi da saukar farashin man fetur kan nahiyar Africa.

Da yake tsokaci game da tasirin rikicin, Dangote ya ce duk da yake lamarin bai shafi Nigeria ba kai tsaye, to amma kuma za ta iya jin tasirin yakin sakamakon yanayin farashin man fetur.

Ya jaddada cewa karuwar farashin makamashi zai shafi kusan kowane bangare na tattalin arziki, abin da ke nufin idan farashin ya ci-gaba da tashi to alumma za su ji a jikinsu.

Dangote ya kuma yi nuni kan yadda rikicin zai shafi lamurran yau da kullum na suniya, ciki har da sauya lokutan aiki da kuma fara aiki daga gida domin rage tsadar makamashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM