Binciken da manema labarai suka gudanar ya nuna cewa, gidan man Ranoil na siyar da lita kan naira 1,370 daga farashin baya na naira 1,440, yayin da Empire Energy ke siyarwa kan naira 1,383 sabanin naira 1,430.
Hakan na nufin cewa gidajen man sun yi ragi na naira 70 da kuma naira 37 kan kowace lita.
Daya daga cikin manajojin gidajen man da ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce sun rage farashin ne domin yin gogayyaya da sauran yan kasuwa.
Rahotanni sun ce kamfanin mai na kasa, NNPCL da MRS suna siyar da mai ne kan naira 1,361 da kuma 1,367.
Lamarin na zuwa ne bayan farashin man fetur ya sauka da kaso 10 a kasuwar duniya zuwa dala 100 kan kowace ganga ga samfurin Brent, yayin da ake siyar da West Texas kan dala 88.85.