Wata kungiyar magoya bayan jamiyyar ADC da ake kira the Grassroot Mobilization Network, ta yi zargin cewa kalaman da shugaban kasa Bola Tinubu ya furta a fadarsa, sun tabbatar da cewa yana da hannu a rikicin da ke faruwa a jamiyyar.A wani bayani da sakataren kungiyar, Idris Bala ya fitar, ya ce kalaman na Tinubu na nuna cewa yana da hannu a rikicin cikin gida dake faruwa a ADC.
Bala ya ce shugaba Tinubu ya yi zargin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na son siye jamiyyar ADC, amma kuma masu ita sun hana shi.
Ya kara da cewa, a dai wannan lokacin, Tinubu ya ce a matsayinsa na dan dimukradiyya, yana shawartar mutane su yi biyayya ga umarnin kotu da tsarin doka.
A saboda haka kungiyar ta ce akwai ban takaici irin wadannan kalaman su fiuto ga babban mutum irin shugaban kasa, kuma hakan na tabbatar da zargin da yan Nigeria suka jima suna yin a cewa fadar shugaban kas ana da hannu a rikicin ADC.