NE

News Elementor

Dakarun Najeriya Guda 200 Zasu Samu Horo A Turkiyya

Najeriya ta sanar da shirin aikewa da jami’an tsaron ƙasar na musamman aƙalla 200 don samun horo a Turkiya ƙarƙashin wata yarjejeniya da ɓangarorin biyu suka cimma, wadda za ta fara aiki cikin gaggawa.

Ministan tsaron Najeriyar Janar Christopher Musa mai ritaya ne ya sanar da wannan mataki bayan tattaunawarsa da takwaransa na Turkiyya Yasar Guler a wani ɓangare na taron diflomasiyyar ƙasar ko kuma Antalya Diplomacy Forum karo na 5 da ya gudana jiya Asabar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa taron na kwanaki 3 ne kuma ana saran halartar ɓangarorin tsaro daga ƙasashe da dama wanda za a yi ƙawance da Turkiyya haɗa ƙarfi don tunƙarar matsalolin tsaro.

Ministan tsaron na Najeriya ya yi bayanin cewa da zarar an kammala taron ne jami’an tsaron Najeriyar na musamman za su isa Ankara don fara karɓar horon bisa buƙatar hakan daga TurkiyaMinistan ya ci gaba da cewa baya ga wannan horo na jami’ai 200 akwai sauran yarjeniyoyin taimakon juna tsakanin Najeriyar da Turkiya a ɓangaren tsaro inda ƙasashen biyu za su ci gaba da aiki tare.

Christopher Musa ya kuma ce Najeriyar da Turkiyya sun amince da haɗa ƙarfi wajen ƙirar wasu kayakin yaƙi da kuma musayar fasaha a ɓangaren tsaro.

Akwai dai alaƙa mai ƙarfi tsakanin Najeriyar da Turkiyya wadda ta faro tun shekarun 1960.

Haka zalika kamar yadda Najeriya ke fama da matsalolin ta’addanci na kusan shekaru 17, itama Turkiya na fuskantar matsananciyar matsalar ta shekaru 40 batun da Christopher Musa ke cewa bisa ga gogewar ƙasar ta Turai ko shakka babu za ta taimakawa Najeriyar wajen magance na ta matsalolin da suka dabaibayeta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM