
Dakarun Brigade ta 17 na Rundunar Sojin Najeriya da ke jihar Katsina sun kuɓutar da mutum shida da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Faskari yayin wani sintiri na yau da kullum.
Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Brigade ta 17, Kyaftin Abayomi Adisa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Katsina.
Ya ce an gudanar da aikin ceton ne a ranar 29 ga Yuni, lokacin da dakarun da ke bakin aiki a Unguwan Doka, yayin wani sintirin ƙafa na yau da kullum, suka tarar da mutanen shida suna yawo cikin daji bayan sun tsere daga hannun masu garkuwa da su.
A cewarsa, waɗanda aka ceto sun haɗa da mata huɗu da yara maza biyu.
Sun haɗa da Misis Umaima Isiaku mai shekaru 30, Amina Isiaku mai shekaru 16, Safiya Isiaku mai shekaru 15, Ramatu Suleiman mai shekaru 30, Muhammad Shehu mai shekaru 4 da Ibrahim Suleiman mai shekaru 2.
Kyaftin Adisa ya ce binciken farko ya nuna cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka yi garkuwa da su daga Unguwan Lado da ke ƙaramar hukumar Kankara a ranar 22 ga Yuni.
Ya ƙara da cewa dakarun sun ba waɗanda aka ceto agajin gaggawa na farko, tare da samar musu da abinci da sauran muhimman buƙatu kafin daga bisani a haɗa su da iyalansu.
Haka kuma, ya ce Kwamandan Brigade ta 17, Birgediya Janar Ishaya Ibrahim, ya sake jaddada aniyar rundunar na ci gaba da gudanar da ƙaimin hare-hare kan masu aikata laifuka.
Ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin da ke ƙarƙashin kulawarta.