NE

News Elementor

Tinubu Ya Fi Kowanne Shugaba Aiwatar Da Aikin Ci Gaban Arewa – Gwamna Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da ayyukan ci gaba a Arewacin Najeriya fiye da kowanne shugaban ƙasa da ya gabace shi.

Uba Sani ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a tashar ARISE Television, inda ya ce gwamnatin Tinubu ta gudanar da manyan ayyuka a fannonin ababen more rayuwa, noma da kiwon lafiya, musamman a jihohin Arewa.

Ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa Arewa ba za ta goyi bayan sake zaɓen Tinubu a 2027 ba, yana mai cewa shugaban ƙasar zai samu ƙuri’u fiye da waɗanda ya samu a zaɓen 2023.

“Ina faɗa ne bisa hujjoji da ƙididdiga. Babu wani shugaban ƙasa da ya yi wa Arewa ayyukan ci gaba kamar yadda Bola Ahmed Tinubu ya yi cikin shekaru uku da suka gabata.” Inji shi

Gwamnan ya ce ɗaya daga cikin manyan ayyukan da ke nuna hakan shi ne aikin titin Abuja zuwa Kaduna, wanda ya ce yana gab da kammaluwa bayan ya daɗe a tsaye.

Uba Sani ya bayyana kwarin gwiwar cewa ayyukan gwamnatin tarayya a Arewa za su ƙara wa Shugaba Tinubu karɓuwa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM