NE

News Elementor

Watanni Tara Bayan Biyan Naira Miliyan 40, Har Yanzu Kwamishinan NSIEC Na Hannun ’Yan Bindiga

Kwamishinan Dindindin na hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Neja (NSIEC), Barrista Ahmed Mohammed, na ci gaba da kasancewa a hannun ’yan bindiga, watanni tara bayan da iyalansa suka biya kuɗin fansa naira miliyan 40 domin neman a sake shi.

An sace Barrista Ahmed ne a ranar 29 ga Satumbar 2025 a kan hanyar Mokwa zuwa Ibbi da ke Ƙaramar hukumar Borgu, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Minna domin gudanar da aikin hukuma.

Lamarin ya faru kusan makonni huɗu kafin zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a jihar Neja a ranar 1 ga Nuwamban 2025.

Wani ɗan uwansa da ya zanta da jaridar Daily Trust ba tare da bayyana sunansa ba, ya ce bayan karɓar naira miliyan 40, masu garkuwar sun sake neman ƙarin naira miliyan 300 kafin su sako shi.

Majiyar ta bayyana cewa a ranar Litinin, ’yan bindigar sun sake tuntuɓar iyalan tare da tambayar ko sun shirya biyan sabon kuɗin fansar, sai dai iyalan sun shaida musu cewa ba su da ikon tara irin wannan kuɗi.

Shi ma wani abokin Barrista Ahmed, Ayuba Abubakar, ya ce iyalan sun yi iya ƙoƙarinsu wajen neman kuɗin fansa tun bayan sace shi, amma har yanzu ba a samu nasarar kuɓutar da shi ba.

Ya kuma bayyana damuwa kan rahotannin da ke nuna cewa lafiyar Barrista Ahmed na ci gaba da tabarbarewa yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutanen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM