NE

News Elementor

APC ta cire tsohon gwamnan Benue Suswam da wasu ‘yan takarar Sanata biyar daga jerin sunayen ƙarshe da ta turawa INEC

Jam’iyyar APC ta cire tsohon gwamnan Jihar Benue, Gabriel Suswam, da wasu ‘yan takarar Sanata biyar daga jerin sunayen ‘yan takarar da ta miƙa wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) na ƙarshe.

Haka kuma, jam’iyyar ta cire tsohon ɗan majalisar wakilai daga Jihar Ondo, Gbenga Elegbeleye, tare da maye gurbin wasu ‘yan takarar majalisar wakilai 19 da suka yi nasara a zaɓen fidda gwani na watan Mayun 2026.

A cikin wasiƙar da shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, da sakataren jam’iyyar na ƙasa, Ajibola Basiru, suka sanya wa hannu, jam’iyyar ta bayyana cewa sauye-sauyen sun biyo bayan rahoton Kwamitin Karɓar Ƙorafe-ƙorafe kan zaɓen fidda gwani.

Jihohin da sauye-sauyen suka shafa sun haɗa da Abia, Kogi, Taraba, Benue, Ebonyi, Ondo, Kaduna, Niger da Kwara.

APC ta kuma tabbatar da sunayen wasu fitattun ‘yan takara, ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Mataimakinsa Jibrin Barau, da gwamna AbdulRahman AbdulRazaq (Kwara), Hope Uzodimma (Imo), Ahmadu Fintiri (Adamawa) da Inuwa Yahaya (Gombe), domin fafatawa kujerun Sanata.

Jam’iyyar ta ce ta karɓi sama da ƙorafe-ƙorafe 700 daga mambobinta kan zaɓen fidda gwani, amma a halin yanzu fifikonta shi ne tabbatar da cewa duk ‘yan takarar sun cike takardun tsayawa takara tare da loda su a manhajar INEC kafin wa’adin 10 ga Yulin 2026.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM