NE

News Elementor

Kotu ta tabbatar da shugabancin David Mark a ADC

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da halaccin shugabancin Sanata David Mark a jam’iyyar ADC, tare da yin watsi da ƙarar ɗan Majalisar Wakilai, Leke Abejide, da ya ƙalubalanci naɗin Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakataren jam’iyyar na ƙasa.

Mai shari’a Musa Liman ya ce kotun ba ta da hurumin shiga harkokin cikin gida na jam’iyya, sannan ya bayyana cewa Abejide bai nuna cewa an tauye masa wata doka ko haƙƙi ba, kuma bai fara amfani da hanyoyin sasanta rikici na cikin jam’iyyar ba kafin ya garzaya kotu.

Kotun ta kuma yanke cewa miƙa shugabancin jam’iyyar daga Ralph Nwosu zuwa David Mark bai saɓa wa kundin tsarin mulkin ADC ba, tare da tabbatar da cewa zaɓen Mark da Aregbesola ya gudana bisa tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar, Dokar Zaɓe ta 2026 da kuma sa ido na hukumar INEC.

Haka kuma, kotun ta umarci Abejide ya biya tarar Naira miliyan biyu ga kowane ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙara, sannan ta ci tarar lauyansa Naira miliyan 10 bisa tanadin Dokar Zaɓe ta 2026.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM