NE

News Elementor

Yan sanda sun daƙile hare-haren ƴan bindiga biyu tare da ƙwato shanu 137 da aka Sace a Sokoto

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto ta bayyana cewa a cikin sa’o’i 48 ta dakile hare-haren ‘yan bindiga guda biyu a Ƙaramar Hukumar Tureta tare da kwato shanu 137 da aka sace a yayin hare-haren.

A cewar sanarwar da Kakakin Rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, ya fitar, jami’an Sashen Yaki da Garkuwa da Mutane, tare da tawaga ta musamman sun kai dauki bayan samun kiran gaggawa daga ƙauyukan Fura Girke da Bimasa da ke kusa da iyakar Jihar Zamfara.

Sanarwar ta ce harin farko ya faru ne a ranar 28 ga Yuni lokacin da ‘yan bindiga suka kutsa cikin ƙauyen Fura Girke, suka rika harbe-harbe tare da sace dabbobin al’umma.

Jami’an tsaro sun garzaya wurin, suka fafata da maharan, lamarin da ya tilasta musu tserewa ta cikin dajin Gizazza, inda suka bar shanu 65 da suka sace.Rundunar ta ce babu wanda ya rasa ransa a harin.

Harin na biyu ya faru ne a ranar 30 ga Yuni a ƙauyen Bimasa, inda wasu ‘yan bindiga suka kai hari, suka rika harbe-harbe babu kakkautawa tare da sace dabbobi.

Rundunar ta ce jami’anta sun yi gaggawar kai dauki, suka yi musayar wuta da maharan, lamarin da ya sa suka tsere zuwa cikin daji tare da barin shanu 72 da suka sace.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Sokoto ya yaba wa jami’an da suka gudanar da ayyukan saboda jarumtaka da ƙwarewar da suka nuna.

Ya kuma buƙaci mazauna jihar su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci domin ƙarfafa yaƙi da aikata laifuka da tabbatar da zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM