
Gwamnatin kasar ta ce ba wata diyya da za ta biya duk wanda ya mallaki wata kadara ba bisa ka’ida ba.
Daya daga cikin ministocin kasar, Khumbudzo Ntshavheni ce ta bayyana hakan, inda ta yi fatali da batun cewa, gwamnatin Pretoria za ta biya diyya ga yan Nigeriar da suka baro kadarorinsu sakamakon rikicin da ya barke a kasar.
Kalaman nata na zuwa ne bayan mukaddashin jekadan Nigeria a Africa ta kudu, Temitope Ajayi, ya ce gwamnatin Nigeria za ta yi kokairn ganin an biya diyya ga mutanen da suka baro kadarorinsu a aksar.
To sai dai, da take mayar da jawabi, Ntshavheni ta ce gwamnatin Africa ta kudu ba ta yi wannan tsarin ba.