
Tuni batun ya haifar da rudani da rikicin cikin gida, inda was uke bayyana shakku kan sahihancin tsarin da jamiyyar ta bi wajan tsayar da yan takara a zaben 2027.
Rahotanni sun ce, kwamitin gudanarwar jamiyyar APC na kasa, ya sauya sunayen mutanen da suka lashe zabukan fitar da yan takara tare da maye gurbinsu da sanatoci 6 wadanda suka sha kaye, bayan kwamitin karbar korafe-korafe ya bada shawarar yin hakan.
Matakin na zuwa ne duk da gargadin da hukumar INEC ta yi na cewa, ba za ta amince da duk wani dan takara wanda ba shi ne ya samu nasara ba a zaben fitar da gwani.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, jamiyyar ta APC ta yi irin wannan sauyi a jihohin Kogi, Abia, Benue, Taraba, Ondo, Niger, Kwara, Kaduna da kuma Ebonyi, inda ta bayar da tikiti ga sanatoci masu ci bayan kuma sun sha kaye a zaben fitar da gwani.