NE

News Elementor

Arewa Ba Za Ta Goyi Bayan Atiku Ba A Zaɓen 2027 Saboda Yanzu Lokacin Kudanci Ne – Ali Modu Sheriff

Tsohon Gwamnan Jihar Borno kuma jigo a jam’iyyar APC, Ali Modu Sheriff, ya bayyana cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ba zai samu goyon bayan Arewa ba a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, yana mai cewa yankin ya yi imanin cewa mulki ya kamata ya ci gaba da kasancewa a hannun Kudu.

Da yake magana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Sheriff ya jaddada cewa ya kamata a mutunta tsarin karɓa-karɓa tsakanin yankunan ƙasar, musamman bayan tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa na shekaru takwas.

Ya ce babu wani dalili da zai sa Arewa ta nemi kujerar shugaban ƙasa a shekarar 2027, yana mai cewa ya kamata Atiku ya dakatar da burinsa har zuwa shekarar 2031.

A cewar Sheriff, shugabannin siyasa sun amince da tsarin rabon mulki tsakanin yankuna ne bayan yaƙin basasar Najeriya domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da tabbatar da adalci tsakanin yankunan ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM