NE

News Elementor

Hadimin Tinubu, Abdulaziz, ya ƙaddamar da shirin ‘Gani Ya Kori Ji’ domin nuna ayyukan shugaban ƙasa

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da kan jama’a, Abdulaziz Abdulaziz, ya ƙaddamar da shirin “Gani Ya Kori Ji” a jihar Kano.

Shirin ya ƙunshi ziyarar duba ayyukan ci gaba a yankuna, da manufar nuna manyan ayyukan more rayuwa da ci gaban da aka aiwatar a Arewacin Najeriya.

Abdulaziz ya ƙaddamar da shirin ne a taron farko na Arewa Media Summit da aka gudanar a Kano.

Ya ce an tsara shirin ne domin cike giɓin da ke akwai wajen isar da bayanai, ta hanyar bai wa ‘yan jarida, masu amfani da kafafen sada zumunta da sauran masu ruwa da tsaki damar ganin ayyukan gwamnati da idanunsu, musamman waɗanda jama’a ba su lura da su ba.

A cewarsa, duk da dimbin kuɗaɗen da gwamnati ta zuba wajen ayyukan more rayuwa da sauran shirye-shiryen ci gaba a Arewacin Najeriya, har yanzu mutane da dama ba su da cikakken bayani kan waɗannan ayyuka saboda ƙarancin yaɗa bayanai.

Ya bayyana cewa shirin zai bai wa ‘yan jarida da masu amfani da kafafen sadarwar zamani damar tantance ayyukan da ake gudanarwa da kansu, sannan su gabatar wa jama’a rahotanni masu inganci da gaskiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM