NE

News Elementor

Dan majalisar dokokin Amurka ya bukaci Najeriya ta Saki Nnamdi Kanu ko a janye mata tallafi

Dan Majalisar Wakilan Amurka mai wakiltar jihar Michigan, John James, ya bukaci gwamnatin Najeriya ta saki jagoran haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ko kuma ta fuskanci yiwuwar rage tallafin da Amurka ke bai wa ƙasar.

James ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar wakilan Amurka, inda ya bukaci a sake gudanar da shari’ar Kanu bisa kundin tsarin mulkin Najeriya da ƙa’idodin kare haƙƙin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa. Ya kuma yi zargin cewa ana tauye haƙƙin Kiristoci a Najeriya.

Dan majalisar ya ce idan ba a saki Kanu ba, ya kamata Amurka ta sake duba tallafin kuɗaɗen da take bai wa Najeriya.

A martaninsa, mai magana da yawun IPOB, Emma Powerful, ya yabawa wannan kira, yana mai cewa hakan na nuna ƙarin hankalin ƙasashen duniya kan shari’ar Kanu.

Nnamdi Kanu na zaman gidan yari bayan da aka yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai a watan Nuwamban 2025 bisa samunsa da laifukan ta’addanci, kuma har yanzu ana jiran sakamakon ƙarar da ya ɗaukaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM