NE

News Elementor

Tsohon hadimin marigayi shugaba Buhari ya ce Peter Obi zai iya ficewa daga NDC kamar yadda ya fice daga LP

Tsohon mai taimaka wa marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan harkokin yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya yi hasashen cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, zai sake komawa wata jam’iyya.

Ahmad ya ce kamar yadda Obi ya yi wa Labour Party, haka zai bar NDC ya koma wata jam’iyya yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2031.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon hadimin shugaban ƙasar ya ce Obi ba zai taɓa ci gaba da zama a jam’iyyar da ba zai iya cimma burinsa na siyasa a cikinta ba.

Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2023 a ƙarƙashin inuwar Labour Party (LP).

A watan Disambar 2025, Obi ya fice daga LP ya koma ADC sakamakon rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar.

Bayan wasu watanni kaɗan, Obi ya sake ficewa daga ADC zuwa NDC, inda ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, tare da Rabiu Kwankwaso a matsayin mataimakinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM