Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya (NPF) ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Olatunji Rilwan Disu, ya umarci jami’an ‘yan sanda da su harbe duk wanda aka samu da bindiga ba bisa ƙa’ida ba.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya kuma mai yaudarar jama’a, tana mai cewa bai wakilci ainihin abin da sufeton yan sandan ya faɗa ba.
Rundunar ta bayyana cewa, a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Makurdi, babban birnin jihar Benue, IGP bai bayar da wani umarnin “harbi nan take” ga jami’an ‘yan sanda ba.
A cewar sanarwar, an cire kalaman Sufeto Janar daga mahallinsu tare da fassara su ta hanyar da ba ta dace ba, lamarin da ya haifar da yaɗuwar bayanan da ba su da inganci.
Saboda haka, Rundunar ‘Yan Sandan ta buƙaci al’umma da su yi watsi da rahoton, tare da tabbatar da cewa jami’anta na ci gaba da gudanar da ayyukansu bisa tanadin doka da ƙa’idojin aiki.