Rahotanni sun ce an sace Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza ne da sanyin safiyar Lahadi a gidansa da ke kan titin Zogirma a Ƙaramar Hukumar Bunza ta Jihar Kebbi.
Majiyoyin da suka zanta da wakilinmu sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na dare, jim kaɗan bayan alƙalin ya dawo daga wata tafiya zuwa Sokoto.
Majiyar ta ƙara da cewa babu wanda ya samu rauni a cikin gidan, duk da cewa maharan sun riƙa harbe-harbe a iska kafin su tafi da alƙalin.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Kakakin ‘yan sandan ya ce bayan samun rahoton sace alƙalin, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, CP Umar Muhammad Hadejia, ya gaggauta tura jami’an rundunonin na musamman da na tattara bayanan sirri domin tabbatar da ceto alƙalin cikin ƙoshin lafiya.