Yunkurin samar da haɗin kan ’yan adawa gabanin babban zaɓen shekarar 2027 ya shiga wani sabon mataki a Nigeria.
Hakan na zuwa ne yayin da wata ƙungiya mai suna G100 ta bayyana cewa ta gudanar da shawarwari da jam’iyyun adawa guda shida, kuma a yanzu tana shirin gudanar da wani babban taro domin ci gaba da tattaunawa kan samar da matsaya guda.
Ƙungiyar ta ce wakilanta sun tattauna da shugabannin jam’iyyar ADC, da APM da NDC da PDP da PRP da kuma SDP.
Ta ce shawarwarin, waɗanda suka haɗa da shugabannin ƙasa na jam’iyyun, ’yan takarar shugaban ƙasa da abokan takararsu, sun haifar da fahimtar juna kan buƙatar jam’iyyun adawa su ƙara haɗin kai da aiki tare.
Wannan na zuwa ne yayin da ya rage saura kwanaki takwas a gudanar da babban taron jam’iyyun adawa da aka shirya gudanarwa a ranar Talata, 18 ga Agusta, 2026, a Abuja.
A cewar G100, ana sa ran taron zai samar da wani dandali da jam’iyyun za su fara cikakken bayani da tattaunawa kan yadda za a samar da ƙarin haɗin kai gabanin zaɓen 2027.
Ƙungiyar, a cikin wata sanarwa da Salihu Mohammed Lukman ya sanya wa hannu a madadin G100, ta ce an gudanar da shawarwarin ne ba tare da fitar da su a bainar jama’a ba, saboda muhimmanci da kuma yanayin batutuwan da ake tattaunawa a kansu.
Ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin bai wa shugabannin siyasa damar yin tattaunawa cikin gaskiya da kuma yanayi mai kyau, ba tare da matsin lambar da ka iya biyo bayan bayyana batutuwan ga jama’a tun da wuri ba.
G100 ta ce shawarwarin da ta gudanar sun biyo bayan wata wasiƙa da ta aika wa shugabannin jam’iyyun adawa a ranar 2 ga Agusta, 2026, inda ta gabatar da abin da ta kira “Doctrine of Necessary Democratic Opposition”, wato “Ka’idar Samar da Adawar Dimokuraɗiyya Mai Muhimmanci.”
Ta ce wannan ka’ida ta ginu ne kan ra’ayin cewa dimokuraɗiyyar Najeriya za ta ƙara ƙarfi idan aka bai wa masu zaɓe wata sahihiyar jam’iyyar adawa wadda za ta iya yin takara yadda ya kamata domin neman amincewarsu.
Ta kuma jaddada cewa ci gaba da rarrabuwar kan jam’iyyun adawa na iya kawo cikas ga ƙoƙarin samar da irin wannan kafa.
Yayin da rahotanni suka nuna cewa shawarwarin sun samar da fahimtar juna kan buƙatar ƙarin haɗin kai, G100 ta amince cewa mayar da wannan fahimtar juna zuwa wani tsari na siyasa mai aiki zai kasance abu mafi wahala.
Saboda haka, ta ce mataki na gaba zai ƙunshi tattaunawa kan hanyoyin da za a bi wajen aiwatar da haɗin kan, ciki har da batutuwan sadaukarwa, sasanci da ɗaukar mataki tare tsakanin jam’iyyun da abin ya shafa.
Ƙungiyar ta jaddada cewa ba za ta yanke hukuncin yadda tsarin zai kasance ba.
Sai dai ta ce aikinta shi ne sauƙaƙa tattaunawa da kuma samar da amincewa tsakanin jam’iyyun.
Ta ƙara da cewa duk wani tsari da za a cimma a ƙarshe dole ne ya yi la’akari da muradu da damuwar jam’iyyun da ke cikin shirin, tare da fifita manyan muradun ’yan Najeriya sama da muradun mutum ko na jam’iyya.
Ƙungiyar ta kuma danganta wannan yunƙuri da ƙa’idojin da ke cikin Ibadan Declaration, musamman kiran da aka yi wa ’yan adawar Najeriya da su samar da sahihiyar hanya da za ta kai ga gabatar da dandamalin siyasa guda, mai ƙarfi kuma mai inganci zaɓen 2027.
Ta ce ba za a iya samun haɗin kai mai ɗorewa ta hanyar tilastawa ba, sai dai ta hanyar tattaunawa da kuma amincewar jam’iyyun da abin ya shafa.
G100 ta ce shawarwarin da aka gudanar a cikin makon da ya gabata su ne farkon abin da ta bayyana a matsayin wani tsari na siyasa mai wahala, wanda ke buƙatar haƙuri, ƙarfin hali da kuma da sadaukarwa.
Ta ƙara da cewa shirye-shirye na ci gaba da gudana tare da wakilan jam’iyyun domin kammala hanyoyin gudanarwa da shirye-shiryen taron da za a yi ranar 18 ga Agusta.
Ƙungiyar ta bayyana kyakkyawan fata cewa fahimtar juna da aka samu a yayin shawarwarin za ta iya zama tushen ƙarin haɗin kai, sai dai ta yi gargaɗin cewa kyakkyawar niyya kaɗai ba za ta wadatar ba.
Ta ce za a ci gaba da gudanar da tsarin bisa tushen haɗa kowa da kuma mutunta juna.
Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan sabon yunƙurin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun kokarin da jam’iyyun adawa da shugabannin siyasa ke yi domin samar da matsaya guda gabanin zaɓen 2027.
Hakan na faruwa ne yayin da ake nuna damuwa cewa ci gaba da rarrabuwar kan jam’iyyun adawa na iya zama wata dama ga jam’iyya mai mulki ta APC.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun nuna cewa rikice-rikicen cikin gida, sauya sheƙa da kuma burin ’yan siyasa daban-daban na neman kujerar shugaban ƙasa na daga cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas ga samar da ƙaƙƙarfan ƙawancen yan adawa.