
An kashe ’yan bindiga 17 da jami’an ’yan sanda 10 a ranar Litinin, yayin da jami’an tsaro suka yi arangama da gungun ’yan bindiga dauke da makamai da ke kokarin shiga Jihar Kebbi daga Jihar Zamfara.
’Yan sanda sun ce fararen hula biyu su ma sun mutu a arangamar da ta faru a yankin Rafin Makuku, cikin ƙaramar hukumar Sakaba ta Jihar Kebbi.
Rahotanni sun ce mazauna yankin sun kiyasta cewa ’yan bindigan sun kai kimanin 240, kuma suna tafiya ne kan babura sama da 200.
An ce sun taso ne daga yankin Sangeko da ke gundumar Dansadau, cikin ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Wani mazaunin Makuku, Malam Musa Sani, ya ce ’yan bindigan sun rabu gida uku, sannan suka yada zango a wani daji da ke tsakanin Kakihum da Makuku, inda suka kwana kafin su nufi Maburya a safiyar Litinin.
Ya ce ’yan bindigan sun yi karo da shingen binciken ’yan sandan tafi-da-gidanka yayin da suke ƙoƙarin shiga garin, inda suka fatattaki jami’an.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi, DSP Bashir Usman, ya ce zuwa yanzu an tabbatar da kashe ’yan bindiga 17 da ake zargi.
A cewarsa, an kuma ƙona babura huɗu mallakar maharan a yayin arangamar, yana mai cewa har yanzu ana ci gaba da tantance adadin waɗanda suka mutu.
Usman ya bayyana jami’an da aka kashe a matsayin jarumai waɗanda suka yi yaƙi cikin ƙarfin hali da kwarewa wajen gudanar da aikinsu.
Ya ƙara da cewa abin da rundunar ta fi mayar da hankali a kai a yanzu shi ne tallafa wa iyalan jami’an da abin ya shafa, kula da waɗanda suka jikkata, da kuma ci gaba da gudanar da ayyukan da za su bi sawun ’yan bindigan da suka tsere