Rundunar ’yansandan Jihar Kwara ta kama wani mutum da ake zargi da kasancewa cikin ƙungiyar masu garkuwa da mutane, yayin da yake ƙoƙarin cire kuɗin fansa da aka biya dangane da sace wasu mazauna ƙauyen Obudu da ke ƙaramar hukumar Ilorin East.
An kama wanda ake zargin, mai suna Muhamodu Sanni, a wani wurin POS, bayan gudanar da bincike na sirri da ya biyo bayan harin da wasu ’yan bindiga suka kai wa al’ummar yankin a ranar 28 ga watan Yuli.
Rundunar ta ce kama Sanni ya kasance wani babban ci gaba a ƙoƙarinta na tarwatsa ba kawai ƙungiyar masu garkuwar ba, har ma da hanyoyin kuɗi da na dabaru da ke taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.
A cewar rundunar, wasu mazauna yankin uku ne aka yi garkuwa da su lokacin da wasu ’yan bindiga suka mamaye al’ummar.
Sai dai lamarin ya sa jami’an bincike faɗaɗa bincikensu, maimakon mayar da hankali kawai kan waɗanda suka yi garkuwar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, kakakin rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce jami’an binciken sun fara bibiyar hanyoyin sadarwa, zirga-zirgar kuɗi da kuma hanyoyin da ƙungiyar ke amfani da su wajen karɓar kuɗin fansa.
Ta ce wannan bincike ne ya kai ga gano Sanni, wanda aka kama yayin da yake ƙoƙarin cire kuɗin da ake zargin yana da alaƙa da kuɗin fansar mutanen da aka yi garkuwa da su.
Rundunar ta ce bayanan da aka samu daga kama Sanni sun taimaka wajen gano ƙarin bayanai kan tsarin ƙungiyar.
Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da binciken cikin sirri, yayin da ake nazari da tantance bayanan da aka samu daga wanda ake zargin, kafin ɗaukar ƙarin matakan aiki.
Kwamishinan ’yansandan Jihar Kwara, Ojo Adekimi, ya tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar za ta ci gaba da kai farmaki kan ƙungiyoyin masu aikata laifuka da kuma hanyoyin da suke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
Kwamishinan ya kuma buƙaci mazauna jihar da su rika bayar da sahihan bayanai cikin gaggawa domin taimakawa jami’an tsaro wajen dakile tare da wargaza ayyukan miyagun ƙungiyoyi.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da ƙoƙarin takaita ayyukan masu aikata laifuka a sassan Jihar Kwara.