NE

News Elementor

Zaɓen Osun Adeleke ya lashe ƙananan hukumomi 19, yayin da Oyebamiji na APC yaci 11

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke na Jam’iyyar Accord, ya lashe ƙananan hukumomi 19 daga cikin 30 na jihar, yayin da babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na Jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ya lashe ƙananan hukumomi 11 a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.


Jaridar PUNCH ta rawaito cewa ana jiran sanarwar hukuma daga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, bayan kammala tattara da bayyana sakamakon zaɓen a ranar Lahadi. Jam’iyyun siyasa 15 ne suka shiga zaɓen, sai dai Accord da APC ne suka fi taka muhimmiyar rawa, yayin da ɗan takarar African Democratic Congress, ADC, Najeem Salaam, ya zo na uku da ƙuri’u 14,989.


Rahoton ya ce a lokacin da PUNCH ta wallafa labarin, ana sa ran Jami’in da ke kula da tattara sakamakon zaɓen jihar, kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar Federal University Oye-Ekiti, Farfesa Joshua Ogunwole, zai bayyana sakamakon ƙarshe a cibiyar tattara sakamakon INEC da ke Osogbo.


Daga cikin ƙananan hukumomin da Adeleke ya samu nasara akwai Boluwaduro, inda ya samu ƙuri’u 7,118, kan 7,050 da APC ta samu, yayin da ADC ta samu 179. A Ede South kuma Adeleke ya samu 26,188, APC 6,219, ADC 390. A Ife North, Adeleke ya samu 13,879, APC 9,613, ADC 333, yayin da a Ilesa West ya samu 16,196, APC 12,756, ADC 673. A Ifedayo kuwa, Adeleke ya samu 7,427, APC 6,836, ADC 115.


A wasu ƙananan hukumomin kuma, APC ta samu nasara. A Ilesa East, APC ta samu ƙuri’u 16,208, yayin da Adeleke ya samu 12,280, ADC 504. A Boripe, APC ta samu 19,963, Adeleke 12,448, ADC 379. A Irepodun, APC ta samu 15,713, Adeleke 14,504, ADC 249, yayin da a Obokun APC ta samu 16,120, Adeleke 12,023, ADC 205.


A sauran wuraren da Adeleke ya yi nasara, ya samu ƙuri’u 12,352 a Orolu, 36,480 a Osogbo, 21,343 a Oriade, da 18,003 a Odo Otin. A Ife East ya samu 27,201, Ifelodun 21,107, Iwo 27,085, Ede North 35,427, sannan Ila 16,211. Sai dai APC ta samu nasara a Atakumosa West da ƙuri’u 10,037, inda Adeleke ya samu 7,479.


A Irewole kuma APC ta yi nasara da ƙuri’u 29,972, yayin da Adeleke ya samu 10,934. A Ayedire, Adeleke ya samu 11,073, APC 9,910. APC ta kuma lashe Atakumosa East da 9,936, yayin da Adeleke ya samu 7,872. A Egbedore, Adeleke ya samu 19,278, yayin da APC ta samu 11,194. A Ayedaade kuma Adeleke ya samu 16,681, APC 15,719, yayin da a Isokan APC ta samu 14,063, Adeleke 13,765.


A Olaoluwa, APC ta samu 10,782, Adeleke 10,063, yayin da a Ife South APC ta samu 14,678, Adeleke 13,507. A Ejigbo, Adeleke ya samu 18,458, APC 16,195, yayin da ADC ta samu 5,053. A Olorunda kuma APC ta samu 24,671, Adeleke 23,514, ADC 666. A cewar PUNCH, sakamakon da aka tattara daga ƙananan hukumomi 30 ya nuna Adeleke ya lashe 19, yayin da Oyebamiji na APC ya lashe 11, amma ana jiran sanarwar ƙarshe ta INEC domin tabbatar da wanda ya lashe zaɓen a hukumance.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM